Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

hukumar rabon arziki ta kasa za ta fara bincikar bankuna game da haraji

Published

on

Hukumar rabon arzikin kasa (RMAFC), ta ce nan gaba kadan ba da dadewa ba, za ta fara bincikar bankuna game da harajin da ake karba akan hada hadar kudi.

 

A cewar hukumar ta na tsammani za ta kwato sama da naira biliyan dari wadanda kudade ne, na haraji da ya kamata ya shiga asusun tarayya.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ibrahim Muhammed ya fitar jiya Lahadi, a Abuja.

 

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan ranar da za a fara binciken ba.

 

Ibrahim Muhammed ta cikin sanarwar ya kuma ce, binciken na kwakwaf zai shafi kudaden haraji na hada-hadar kudi da wasu bankuna ashirin da biyu suka karba daga shekarar dubu biyu zuwa dubu biyu da goma sha takwas.

 

Sanarwar ta kara da cewa, bankunan kasuwancin kasar nan suna ciran ladar naira hamsin a duk ajiya da abokin huldar su yayi  a asusun ajiyar sa da ya kai naira dubu daya ko sama da haka, kuma hakan na wakana tun a shekarar dubu biyu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!