Labarai
Hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta sallami jami’anta dari da goma sha biyar daga aiki

Hukumar tsaro ta DSS ta ce ta sallami wasu jami’anta dari da goma sha biyar daga aiki.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, a ranar Talata, DSS ta bukaci al’umma su kaucewa mu’amala da jami’an a matsayin wakilan hukumar.
Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kore su ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.
Matakin na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama wasu tsoffin jami’anta biyu bisa zargin amfani sa sunan hukumar suna damfarar mutane.
You must be logged in to post a comment Login