Kiwon Lafiya
Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta cafke tsohon babban daraktan DSS Ita Ekpeyong
Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta cafke tsohon babban daraktan hukumar tsaron farin kaya DSS Mista Ita Ekpeyong, da yammacin yau alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta cafke Mista Ita Ekpeyong ne a gidan sa mai lamba 46, kan titin Maman Nasir, da ke Unguwar Asokoro, a birnin tarayya Abuja.
Da tsakar ranar yau Alhamis ne dai aka ga jami’an na EFCC a cikin motocin bas uku sun yiwa gidan kawanya bisa rakiyar jami’an yan sanda 20 dake da makamai.
Jami’n sun rika shiga lungu da sako na gidan suna bincike, kafin daga bisani da karfe 3 da mintuna 20 suka fice daga gidan, inda suka yi awun gaba da tsohon daraktan na DSS.
Rahotanni sun ce babu dai wasu tsabar kudi da aka gano yayin binciken, kuma wannan sumame na zuwa ne kusan watanni 10 bayan da jami’an na DSS karkashin korarren daraktan ta Lawal Daura suka suka hana EFCC gudanar da bincike a gidan na Ekpeyong duk kuwa da umarnin kotu kan batun.
Rahotanni sun kuma mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ne ya bada umarnin sumamen na dazu bayan da ya gana da mukaddashin shugaban na EFCC Ibrahim Magu da kuma sabon shugaban na DSS Matthew Seyifa, jiya Laraba.