Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kasar Ghana ta sallami ministan makamashinta daga aiki

Published

on

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya sallami ministan makamashin kasar daga bakin aiki.

Wani bayani daga fadar shugaban kasar na cewa an umarce shi da ya mika wa ministan filaye da ma`adinan kasar mukamin sa wanda zai yi rikon kwarya kafin a nada sabon ministan.

Sallamar ministan makamashin Mista Boakye Agyarko ta fara aiki a nan take bayan fitowar wata ‘yar gajeriyar sanarwa, dauke da rattaba hannun daraktan sadarwa na fadar shugaban kasa Mista Eugene Arhin.

Duk da yake babu wani dalili da aka bayar na sallamar ministan daga aiki, amma masu sharhi na zargin hakan ba ya rasa nasaba da yarjejeniyar makamashi ta Ameri, wadda aka shiga tun lokacin tsohowar gwamnatin NDC, wadda kuma jam`iyya mai mulki ta NPP ta yi ta suka tare da shan alwashin soke ta da zarar ta hau mulki.

Ministan makamashin ya fara shan matsin lamba ne tun bayan da ya yi ikirarin yunkurin sake sabunta yarjejeniyar ta Ameri, kan hujjar cewa ta fi wacce aka kulla a baya.

Sai dai wasu manyan jami`an hukumar samar da makamashi Volta River Authority suna gardamar cewa, ikirarin da ministan ya yi na kebe wa Ghana dala miliyan hudu saboda sabunta yarjejeniyar ba shi da tushe bare makama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!