Labarai
Hukumar zaɓe ta kano ta sanya ranar zaɓen ƙananan hukumomi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta ce zata gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar a ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2024 domin bawa ƙananan hukumomi damar cin gashin kan su da kotu ta bayar da umarni.
Shugaban hukumar Farfesa Sani lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan da safiyar yau yayin taron manema labarai da ya gudana a ofishin hukumar.
Farfesa Malumfashi ya kuma tabbatar da cewa za’a ko wace jam’iyya da take shirin yin takara, za’a fara yakin neman zaɓen a ranar 1 ga watan Nuwambar.
Haka kuma shugaban hukumar ya tabbatar da cewa duk wani ɗan takara da aka samu da sanya fastar sa a gidan gwamnati ko masarauta zata sauke shi daga jerin ƴan takara.
Hukumar ta ce zata fara shirye-shiryen fara gudanar da zaɓen a ranar 15 ga watan Agusta inda shugaban hukumar yace za’a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da nufin ayyana duk wanda ya sami nasarar lashe zaben.
You must be logged in to post a comment Login