Labarai
Hukumomi kadai ba za su iya magance cin hanci da rashawa ba- EFCC
Majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar tara ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta Duniya.
Yayin da ta bayyana cewa a duk shekara ana sallawantar da dalar Amurka Tiriliyon daya wajen aikata cin hanci da rashawa, kuma da ake sace dallar amurka tiriliyon biyu a fannin cin hanci da rashawa.
Kazalika majalisa ta ce cin hanci da rashawa na daya daga cikin abin da ke lalata zamantakewar mutane da tattalin arzikin kasa, zaman lafiya da kuma tabarbarewar al’umma.
Haka zalika cin hanci da rashawa na daya daga cikin abin da ke lalata zaman takewar mutane, kawo rashin samaun ci gaban daya kamata ga gwamnati.
Kano:Hukumar cin hanci da rashawa ta jihar ta kwato fiye da naira biliyan 4
Hukumar shige da fice ta ja kunnen wasu jami’anta kan cin hanci
Hukumar shige da fice ta ja kunnen wasu jami’anta kan cin hanci
Majalisar ta dinkin Duniya ta ware ranar tara ga watan dicambar kowacce shekara a matsayin ranar yaki da cin hanci da rashawa inda take fadakar da al’umma game da illar da cin hanci da rashawa ke da shi.
Ranar dai na da nufin yin gangami da kuma gudanar da jawabi, baya ga wayar da kan mutane kan illar cin hanci da rashawa da kuma alfanun guje masa.
Wakilin Freedom Radiyo Abubakar Tijjani Rabiu ya zanta da wasu mutane a kwaryar birnin Kano, game da muhimmancin ranar tare da bayyana ra’ayoyin su kan yadda za’a iya magance cin hanci da rashawa a kasar nan.
Da yake jawabi yayin gangamin da hukumar ta EFCC reshen jihar Kano ta gudanar a yau Shugaban sashin sanya idanu kan yadda gwamnati ke kashe kudade Sunusi Aliyu Muhammad cewa yai hukumomi kadai ba zasu iya magance cinhanci da rashawa ba a kasar nan adon haka dole al’umma sai sun taimaka wajen kayar sa.
Kwamared Akibu Hamisu Garko shine Shugaban ci biyar wayar da kan Jama’a kan illar cin hanci da rashawa a Africa wato African center for transparency and anti-corruption advocacy, cewa yai babban abinda ke kara ta’azzara cin hanci da rashawa a kasar nan shine rashin fitar da bayanai na abinda gwamnati ke kashewa a ayyukan da take gabatarwa ga jama’a, wanda ta hakane kawai za’a iya magance rashawa ga Hukumomin gwamnati a kasar nan.
Taken bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta wannan shekara shine”rufe kowacce kofa da zata bada damar karba ko kuma bayar da cin hanci’’