Labarai
Kano:Hukumar cin hanci da rashawa ta jihar ta kwato fiye da naira biliyan 4
Hukumar Kula da Laifukan Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano ta ce ta kwato fiye da naira biliyan 4 da wasu kadarori daga wajen wasu al’umma da suke yi wa tattalin aziki zagon kasa a jihar Kano a shekaru hudun da suka wuce.
Shugaban hukumar Barista Muhiyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya .
Bari. Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce tun bayan da ya fara aiki a ofishin hukumar ta samu damar sauraron korafai-korafan daga wajen kimanin mutane dubu goma sha hudu, haka nan kuma sun sami wasu sauraron korafai-korafai daga wajen wasu unguwanni guda dubu hudu.
Idan za’a Iya tunawa dai gwamnan Kano Abdullahi umar Ganduje ya nada Muhiyi Magaji Rimin Gado a Yunin shekara ta 2015 a matsayin shugaban hukumar cin hancin da rashawa ta jihar Kano.
Ayyukan hukumar dai sun hadar da binciken ofisoshin ‘yan siyasa da wasu manyan ma’aikatan gwamnati ba tare da jin tsoro ko fargaba ba kamar yadda Muhuyi Magajin ke bayyanawa.