Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukuncin kisa ne ya fi dacewa ga masu yin ɓatanci – Amb. YY Hamza

Published

on

Jarman matasan Arewa Ambasada Hamza Yunusa Yusuf ya ce aiwatar da hukuncin kisa ga masu yin ɓatanci ga addini shi ne zai kawo ƙarshen masu aikata wannan mumunar dabi’a.

Ambasada Yunusa ya bayyana hakanne a wata zantawa da Freedom Radio kan makomar matasa a rayuwa.

Ya ƙara da cewa, tilas ne mahukunta su yi ƙoƙari wajen ganin an inganta rayuwar matasa ta yadda za su rika yin tunani mai kyau.

Ambasa ya ce, rashin samun kyakkyawar tarbiyya su ne ke jefa matasa cikin munanan aƙidu da kan kai su ga yin ɓatanci ga addini.

A ƙarshe ya nemi gwamnatin Kano da ta aiwatar da hukuncin kisa ga matashinnan da kotu ta yanke wa hukunci a Kano sakamakon yin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta (s.a.w).

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!