Labaran Wasanni
Hukuncin kotu ba zai hana mu lallasa Madrid ba – Guardiola
Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola yace a shirye kungiyar take data gabatarwa da kotu hujjojin dake nuna cewa kungiyar Bata karya dokokin hukumar kwallon kafar turai ba wanda ya Sanya kotu yanke Mata hukuncin shekaru biyu daga buga gasar zakarun turai ta Champion league.
A yau laraba ne dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester City zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Spaniya a zagayen farko na kungiyoyi 16.
Wasan da zai gudana a filin Wasa na Sentiago banabaur dake kasar Spaniya.
Hukumar ta UEFA na tuhumar Manchester City da kin rashin bayyana kudaden datake samu na tallace-tallace da kuma kudaden da take kashewa.
Sai dai tun lokacin da kotun ta yankewa City hukuncin ta bata damar daukaka Kara idan bata amince da hukuncin data yanke mataba.
Pep Guardiola ya ce adon haka kungiyar zata daukaka Kara Kan hukuncin da kotun ta yanke mata.
A cewar sa idan har kungiyar ta Manchester City ta can canci buga gasar a kakar wasanni mai zuwa babu abinda zai hanata zuwa gasar, adon haka hukuncin da kotun ta dauka Kan kungiyar ba zai tasiriba.
Pep Guardiola, dai ya ciwa tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona kofin zakarun na Turai sau biyu sai dai tin zuwansa kungiyar ta Manchester City bai taba kaika wasan kusa dana kusa da karsheba.
Guardiola ya ja hankalin Yan wasan kungiyar da kada hukuncin da kotu ta dauka na dakatar da kungiyar shekaru biyu na zuwa gasar ta zakarun turai yasa su karaya a wasan da zasuyi da Real Madrid a daren yau.
Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu
Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana
‘Yan wasan Nigeria na ci gaba da taka rawar gani a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai
Akwanakin baya dai Guardiola ya fito yayi wata magana cewa yana da tabbacin cewa idan ya kasa cire Real Madrid a gasar ta zakarun turai kungiyar zata iya korarsa.
Rahoto: Abubakar Tijjani Rabi’u
You must be logged in to post a comment Login