Connect with us

Labaran Wasanni

Yanzu yanzu an dakatar da wasan Real Madrid da Manchester City

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa, ta dage wasan gasar zakarun nahiyar turai,wato  Champions league, zagaye na biyu na wasan da za’a fafata tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester city da Real Madrid, da za’ayi a kasar Ingila a mako mai kamawa sakamakon barkewar cutar Coruna Virus.

Kungiyar Manchester city, ce ta amince da hakan tare da hadin gwiwa da hukumar kwallon kafa ta Uefa, bayan da Madrid ta killace wasu ‘yan wasan ta don binciken lafiyar su bayan bullar cutar a cikin tawagar ‘yan wasanta na kwallon Kwando wato Basketball.

Labarai masu alaka.

Hukuncin kotu ba zai hana mu lallasa Madrid ba – Guardiola

An dakatar da wasan Tennis saboda barazanar cutar codiv 19.

Shima wasan Juventus, da Lyon,an dage shi zuwa wani lokacin bayan da dan wasan bayan kungiyar Daniele Rugani, ya kamu da cutar mai lakabin COVID-19,  wanda hakan ya sa tawagar  ta killace shi don cigaba da duba lafiyar sa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,149 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!