Labarai
Hukuncin kotun koli na jihar Imo, ya janyo zaman dar-dar a Kano
Daga Abdullahi Isah.
A jiya Talata ne kotun kolin kasar nan ta yanke hukuncin, soke nasarar da gwamnan jihar Imo Emeka Ehedioha ya samu a zaben gwamna da ya gudana a jihar a watan Maris din shekarar da ta gabata.
A cewar kotun hukumar zabe ta kasa INEC ba ta kyauta ba da ta soke sakamakon wasu rumfunar zabe dari uku da tamanin da takwas. Sakamakon da ke nuna cewa Dan takarar jam’iyyar APC Sanata Hope Uzodinma shi ke kan gaba da gagarumin rinjaye a yankunan.
Tun bayan da kotun ta yi wannan hukunci al’ummar kasar nan ke ta bayyana mabambantan ra’ayi kan batun.
Sai dai ni wanda ya fi daukar hankali na shine wanda alummar jihar Kano da masu fashin baki ke yi game da hukuncin kotun kolin wanda suke alakantashi da abinda ka iya faruwa a hukuncin da kotun za ta yi a ranar litinin 20 ga wannan wata da muke ciki na Janairu.
To koma ma me zai faru masu lura da lamuran yau da kullum na ganin cewa hukuncin kotun kolin na jiya ya janyo Zaman dar-dar a Kano sakamakon cewa kowane bangare da ke jayayya kan shari’a na ganin cewa lamarin ka iya shafar su, ko dai su yi nasara ko Kuma akasin haka.
Ba ko shakka ga mu masu kallon lamarin daga bayan fili zamu fi ganin lamarin daban da yadda su masu tankiya da junan ke kallon lamarin.
Masana harkokin Sharia dai na ganin cewa matukar kotun kolin ta kalli zaben da ba a kammala ba wato inconclusive a matsayin haramun to fa ba ko shakka bangaren gwamnati da ke mulki yanzu suna ruwa domin hakan zai nuna kenan abokin takararsu na jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf shine wanda za a sanar a matsayin wanda ya samu nasara a zaben.
Bugu da kari masu kallon lamarin ta wani bangare kuwa suna kallon cewa ai tunda kotun a yayin yanke hukuncin jihar Osun ba ta ce zaben na Inconclusive haramun bane, to kuwa ba za ta sauaya ra’ayi kan na Kano ba.
Koma me zai kasance bako shakka yanzu cikin wasu ya debi ruwa.
‘Yan siyasa kuma yanzu jinin su ya hau, za su Kuma ci gaba da zaman dar-dar daganan zuwa ranar litinin mai zuwa ranar da Kotun Koli za ta yanke hukunci.
Mu dai namu ido muna dai Kuma fatan koma me zai faru jihar Kano za ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da yalwar arziki.
Rubutu daga Abdullahi Isah