Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

ICPC ta kama mutane 4 bisa zargin su da sayen kuri’a

Published

on

Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce, jami’anta sun kama mutane huɗu bisa zargin su da sayen ƙuri’a yayin zabe a jihohin Sokoto da Katsina.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce, ta kama mutanen ne jiya Asabar a yayin da ake gudanar da zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.

Haka kuma hukumar ta ce, an kai wa jami’anta hari tare da raunata mutum guda a jihar Sokoto.

ICPC ta ce an kai wa jami’an nata harin ne a daidai lokacin da ta kama mutum uku masu sayen ƙuri’a a zaɓen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!