Connect with us

Labarai

ICPC ta kara tsare Nasir El-Rufa’i

Published

on

Hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta sake kama tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, bayan da aka kasa kammala sauraron buƙatar belinsa a kotun tarayya da ke Kaduna. Alkalin kotun, Mai shari’a Rilwan Aikawa, ya ɗage shari’ar zuwa ranar Laraba domin ci gaba da sauraron bukatar.

Jinkirin ya biyo bayan sabbin muhawara da ƙorafe-ƙorafe tsakanin ɓangaren masu gabatar da ƙara da kuma lauyoyin El-Rufai.

 

Tun da fari, ɓangaren tsaro ya nemi alkalin ya janye kansa daga shari’ar bisa zargin son rai, amma daga bisani suka janye wannan buƙata, lamarin da ya haddasa tsaiko a shari’ar.

Ana tuhumar El-Rufai da laifuffuka da suka haɗa da karkatar da dukiyar jama’a da sauran al’mundahar kuɗi, ciki har da zargin karɓar sama da Naira miliyan 289 a matsayin alawus da ya zarce haƙƙinsa, da kuma kusan dala dubu 797 da ake zargin kudin haram ne.

 

Bayan zaman kotun, jami’an ICPC suka kara tsare shi, yayin da aka tsaurara tsaro a harabar kotun tare da hana ‘yan jarida shiga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!