Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta fara sauraron shari’ar maita a Kaduna

Published

on

Al’ummar yankin Doka dake kasuwar magani a jihar Kaduna sun shigar da karar wani mutum mai suna Alla Magani da suke zargi da maita.

Rahotonni  sun bayyyana cewa,  an fara sauraron karar a kotun majestiri dake unguwar Barnawa karkashin mai shari’a Abdul’aziz Ibrahim Kagarko, a yau Laraba.

A yayin zaman kotun an karantowa wanda ake zargin abinda ake tuhumarsa  da aikatawa na cinye kurwar wata yarinya ta hanyar maita, kuma babu musu ya amsa laifinsa nan take.

Labarai masu alaka

Hukumar korafe korafe na binciken Alkalan Kotun Majistret

Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano

Ana zargin sarakunan mayun Kano na bogi ne

Wakilinmu Haruna Ibrahim Idris ya rawaito mana cewa mai shari’a Abdul’aziz Ibrahim Kagarko ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu  mai kamawa domin gabatar da shaidu daga bangaren masu kara.

Kazalika Alkalin ya aike da wanda ake zargin zuwa gidan ajiya da gyaran hali har zuwa ranar da za’a cigaba da shari’ar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!