Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Rana

ICPC-Zamu binciki kwantiragin asusun ƴan sanda na sama da biliyan 11

Published

on

Hukumar yaƙi da cin hanci da almundahanar kudade ta ƙasa ICPC, ta fara binciken kudaden kwantiragi na sama da biliyan 11 na asusun fanshon ƴan sanda na ƙasa.

A wata takarda da daraktan gudanar da aiyyuka na hukumar Akeem Lawal, ya sakawa hannu tare da aikewa da tsohon shugaban ‘yan sanda na ƙasa Suleiman Abba.

Sannan kuma an aikewa da wasu manyan muƙarraban hukumar bakwai da su bayyana a gabanta.

Sauran wanda aka gayyata sun hada da uwargida Victoria Ojogbane, da Alhaji Yahaya Mohammad, sai Lawal Gujungu,da Salihu Abubakar, sai Femi Akinfala, da Ben Akabueze, da Mansur Hammed.

Hukumar ta buƙace su da su bayyana a gabanta tun daga ranar 13 ga watan Satumbar shekarar 2021, zuwa lokacin da zata cigaba da gudanar binciken a wa’adin ranakun data dauka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!