Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Jam’iyyar YPP ta kori  jagoran jam’iyyar daga mukamin sa

Published

on

Majalisar zartaswar jamiyyar Youth Progressive Party YPP ta jihar Kano ta kori tsohon shugaban jamiyyar na riko Ibrahim Sadauki Kabara sakamakon zargin cin Amana da rashin gaskiya da saba dokokin jamiyyar.

Barista Salisu Salisu Umar , ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar , yana mai cewa majalisar zartaswar jamiyyar ta dauki matakin  ne biyo bayan saba dokokin jamiyyar da tsohon shugaban yayi wanda kuma ya saba da kundin tsarin mulkin jamiyyar.

Majalisar zartaswar jamiyyar ta kuma amince da nada Barista Salisu Salisu Umar a matsayin sabon shugaban na Jihar Kano domin dorawa daga inda aka tsaya.

Kotun sauraron korafin zabe ta ki amincewa da bukatar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP

OSUN:kotu ta karyata ikrarin jam’iyyar PDP

Taraba:Darius Ishaku na jam’iyyar PDP ya lashe zabe

Barista Salisu Salisu Umar ya kuma shawarci matasa da kada su bari ‘yan siyasa marasa kishi suna amfani dasu wajen tayarwa da jama’a hankali lokacin yakin Neman Zabe , dama amfani dasu wajen zabar mutanan da basu kamata ba domin sune ke jefa kasar nan cikin mawuyacin hali.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Barista Salisu Salisu Umar na shawartar al’ummar Kano da su cigaba da adduar neman dorewar dimukaradiyya a fadin kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!