Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina buƙatar sanin shari’o’i masu cin karo da juna da aka gudanar – CJN Tanko Muhammad

Published

on

Babban jojin ƙasa mai shari’a Tanko Muhmmad ya buƙaci a gabatar masa da bayanan hukunce-hukuncen shari’o’i masu cin karo da juna da aka zarta  a kotunan ƙasar nan.

Mai magana da yawun hukumar sharia ta  ƙasa Soji Oye ne ya tabbatar da hakan.

Soji Oye ya ce, manyan alƙalan jihohin Rivers, Kebbi, Cross Rivers, Anambra, Jigawa da Imo za su gana babban Jojin a Litinin ɗin nan.

A cewar sa, za su gana ne domin amsa tambayoyi kan umarni kotu na wasu shari’o’i masu rikitarwa da aka bayar a jihohin su daban daban.

Wannan ya biyo bayan yadda aka samu rikice-rikicen cikin gida a manyan  jam’iyyun siyasar ƙasar nan a baya-bayan nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!