Labarai
Ina daga cikin mutanen da masu shirin juyin mulki ke son kamawa- Ministan Tsaro

Ministan Tsaron ƙasar nan Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa yana daga cikin mutanen da masu shirin juyin mulki suka sa a jerin waɗanda za a kama ko a hallaka idan suka ƙi bin umarni su.
Christopher Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels, bayan rundunar soji ta tabbatar da cewa an bankado yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Janar Christopher Musa ya ƙara da cewa shi kansa an shirya kama shi, kuma idan ya ƙi, za a kashe shi, inda Ya ƙara da cewa wasu manyan jami’an gwamnati suma na cikin jerin mutanen da aka yi niyyar hallakawa.
Sai dai Tun a watan Oktoba ne aka kama wasu sojoji daga matakin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar bisa zargin shirya juyin mulki.
Inda Rahotanni suka nuna cewa kwamitin bincike ya mika sakamakon bincikensa ga Shugaban ƙasa, kuma za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotun soja.
You must be logged in to post a comment Login