Labarai
Ina goyon bayan bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai – Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci majalisun dokokin tarayya da su gaggauta ayyana dokar da za ta bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai.
A cewar tsohon shugaban kasar kamata ya yi dokar ta bai wa kananan hukumomin ‘yancin neman kudaden shiga da kansu.
Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke zantawa da shugabannin kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE wadanda suka kai masa ziyara gidansa da ke garin Otuoke a jihar Bayelsa.
Tsohon shugaban kasar ya ce da shi dan majalisa ne da abin da zai yi shine neman goyon bayan abokansa don bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai.
A cewar Jonathan al’ummar da ke yankunan kananan hukumomi suna da ‘yancin amfana da dukiyarsu, a don haka ba daidai bane dukiyoyinsu su rika makalewa a jihohi.
You must be logged in to post a comment Login