Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ina yabawa ‘yan sandan jihar Kano –Magajin garin Daura

Published

on

A yau Talata ne magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba ya kawo ziyara wurin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP. Ahmed Iliyasu inda ya yaba musu bisa jajircewa matuka wurin aikin su.

Idan zaku iya tunawa dai a ranar 1 ga watan Yulin wannan shekarar da muke ciki ne ‘yan bindiga suka sace magajin garin wanda ya shafe tsawon watanni 2 a hannunsu, kafin daga bisani ‘yan sanda suyi nasara ceto shi a nan birnin Kano.

Hotunan magajin garin Daura tare da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina dai ta sanya tukuicin kudi har miliyan biyar ga duk wanda ya gano inda yake a wancan lokacin.

Lokacin da ‘yan sanda suka tseratar da magajin garin Daura

RUBUTU MASU ALAKA:

Rundunar yan sandan Kano ta kubutar da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar

Kano: Yan sanda sun kama wani da ake zargin dan Boko Haram

Yadda ‘Yansandan Kano suka cafke wadanda suka kone magidanci

Shugaba Buhari ya gana da sufeton yan sanda ta kasa kan arangamar yan Shi’a

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!