Kaduna
Inconclusive: An shiga ruɗani a Kaduna bayan hukuncin kotu
Rahotanni na nuna cewa an shiga ruɗani a jihar Kaduna bayan sanar da hukuncin Kotu kan zaɓen gwamna.
Freedom Radio Kaduna ta tawaito cewa, a halin yanzu dukkanin ɓangarorin na gudanar da shagulgulan murna a matsayin sune suke da nasara.
Kazalika a ɓangaren lauyoyin da ke kare ɓangarorin biyu sun shiga ruɗani bisa rashin takamaiman hukuncin da aka dogara a kan sa.
Sai dai lauyan jam’iyyar PDP Barista Baba Lawal Aminu ya ce “A kotun alƙalai uku ne a ciki, biyu daga ciki suka bada umarnin aje a sake zaɓe a mazaɓun da ake zargin an samu maguɗi, yayin da alƙali ɗaya ya ce ya tabbatar da gwamna mai ci a matsayin wanda ya samu nasara, saboda haka ita Shari’a majority wato mafi rinjaye ake tafiya a kanta.”
A bangaren lauyan jam’iyyar APC Barista Sunusi Musa kuwa ya ce “Kotu ta kori ƙarar gaba ɗaya daga gabanta sakamakon rashin gamsassun hujjoji da jam’iyyar PDP ta gabatar, don haka yanzu ba batun sake zaɓe har sai in jam’iyyar PDPn da ɗaukaka ƙara.
Wannan ne ya nuna cewa akwai ruɗani game da hukuncin da aka yanke, sakamakon yadda ɓangarorin biyu ke ganin sune da nasara, a gefe guda kuma magoya bayan su na ci gaba da murna.
You must be logged in to post a comment Login