Labarai
INDA RANKA: Majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin bincike kan karɓar kuɗaɗen ɗalibai
Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa Kwamitin bincike game da koken ɗaliban makarantar Health Technology na cewa ana karɓar musu kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Hakan ya biyo bayan ƙudirin gaggawa da Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Doguwa Salisu Ahmed ya gabatar a zaman majalisar na yau Talata.
Ɗan Majalisar ya ce, ya saurari ƙorafin ɗaliban a shirin Inda Ranka na Freedom Radio, wanda hakan ya ja hankalinsa.
Salisu Ahmed ya nemi majalisar da ta binciki su waye ke da alhakin karɓar kuɗin ɗaliban, domin hakan zai kawo naƙasu a harkar ilimi.
Shi ma Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Rimin Gado da Tofa, Muhammad Bello Ɓutu-ɓutu ya yi ƙarin haske a kai.
Ya ce, kashi 70 zuwa 80 na ɗaliban da suke karatu ƴaƴa ne da suka fito daga gidajen marasa ƙarfi, don haka ya zama wajibi ga majalisa ta binciki al’amarin.
A ƙarshe Majalisar ta amince da wannan ƙudiri na gaggawa inda ta kafa Kwamiti ƙarƙashin Kwamitoci ilimi dana lafiya tare ba su wa’adin makonni biyu su kawo rahotonsu.
You must be logged in to post a comment Login