Connect with us

Labarai

India da wasu kasashe sun ki amincewa da jakadun Najeriya

Published

on

Wasu ƙasashe da suka haɗa da India sun ƙi amincewa da wasu jakadun da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa, saboda dokar diflomasiyya da ke hana karɓar jakadu daga gwamnatin da ta rage mata ƙasa da shekaru biyu a kan mulki.

Rahotanni sun nuna cewa Muhammad Dahiru, wanda aka tura ya zama jakadan Nigeria a kasar Indiya, na iya fuskantar ƙin amincewa saboda wannan doka.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, jami’ai a fadar shugaban ƙasa da ma’aikatar harkokin waje sun ce wasu ƙasashe na nuna alamun ba sa son ba da izinin da ƙasa ke bayarwa kafin jakadan wata ƙasa ya fara aiki.

Sun bayyana cewa wasu ƙasashe suna ganin gwamnatin Tinubu na gab da karewa, domin zaɓen shugaban ƙasa na gaba da hukumar zabe mai zaman kanta a a Najeriya INEC ta tsara zai gudana a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da wa’adin farko na Tinubu zai ƙare a Mayu 2027.

 

Sai dai a iya cewa wannan lamari na iya haifar da koma baya a al’amuran Diflomasiyya tsakanin Najeriya da sauran kasashen Duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!