Labarai
INEC: ta bijiro da salon tsari na baiwa masu bukata ta mussaman damar zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da bijiro da wani sabon tsari da zai baiwa masu bukata ta musamman da sauran al’umma damar yin zabe ba tare da fuskantar wani cikas ba.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmoud Yakubu wanda ya samu wakilcin Kwamshina a huumar Dokta Adekunle Ogunmola wajen kaddamar da sabon tsarin a jiya Talata, a birnin tarayya Abuja, ya ce sun bullo da tsarin ne don baiwa kowa damar shiga a dama da su a harkokin zaben kasar nan.
Dokta Ogunmola ya ce cikin tsarin akwai tanadin yadda masu bukata ta musamman za su samu damar yin zabe, suma a zabe su tare kuma da rike mukamin siyasa kamar kowa.
A jawabinta Ministar harkokin mata Sanata Aisha Alhassan ta ce ma’aikatar ta za ta hada gwiwa da INEC don tabbatar da ganin an tabbatar da wanzuwar wannan tsari ba tare da muzgunawa kowa ba.
Ministar ta kara da cewa Najeriya tana da mutane masu bukata ta musamman sama da miliyan goma, wadanda akasarinsu sun kai matakin yin zabe.