Labarai
INEC ta fitar da sunayen ƴan takarar ƙananan hukumomin Abuja

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta fitar da sunayen ƙarshe na ‘yan takarar da za su fafata a zaɓen ƙananan hukumomi na Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka shirya gudanarwa ranar 21 ga Fabrairun shekarar 2026 da ke tafe.
A sanarwar da kwamishinan hukumar mai kula da wayar da kan masu kaɗa kuri’a Sam Olumekun, ya fitar, ya ce, jam’iyyun 17 ne suka cika dukkan sharudda kafin ranar 11 ga Agustan shekerar nan da muke ciki ta 2025, lokacin da aka rufe yin rajistar wadanda za su shiga takarar.
Haka kuma Hukumar ta bayyana cewa jerin sunayen ya haɗa da ‘yan takara na kujerun shugabancin ƙananan hukumomi da mataimakansu, tare da ‘yan takarar kujerun majalisun ƙananan hukumomi.
INEC ta kuma ja hankalin jam’iyyun siyasa cewa bayan sakin wannan jerin, babu damar janye ko sauya ‘yan takara sai dai idan ɗan takara ya rasu kafin ranar zabe, kamar yadda doka ta tanada.
Zaɓen na Abuja dai zai kasance babban gwaji na farko a shekarar 2026, kafin babban zaɓen jihohi da na tarayya da ke tafe a shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login