Labarai
INEC ta ja kunnen masu mallakar rijistar zabe fiye da 1

Hukumar zabe mai zaman kanta Najeriya INEC shiyyar Kano, ta ja kunnan mutanen da suka san suna da rijistar zabe da su guji zuwa domin sake yin wata.
Mai magana da yawun hukumar ta INEC shiyyar Kano Nahila Bello Dandago, ce ta bayyana hakan a zantawarta da wakilinmu Abubakar Tijjani Rabi’u.
Ta kuma bayyana cewa, duk wanda ya mallaki katin yin zaben guda biyu, to zai rasa katin nasa gaba daya.
Haka kuma, ta kara da cewa, duk a inda mutum ya ke a fadin Najeriya zai iya yin Rijistarsa kuma ya karbi katin a karamar hukumarsa.
You must be logged in to post a comment Login