Labarai
INEC ta karbi koken al’umma kan haduwar rankun zaben 2027 a watan Azumi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa tana duba koken da aka gabatar kan haduwar ranakun zaben 2027 da watan Azumin Ramadan.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da shugaban kwamitin yada labaran hukumar, Malam Mohammed Kudu Haruna ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa an tsara jadawalin zaben ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin 1999 da aka gyara, dokar zabe ta 2022 da kuma ka’idojin INEC, inda aka sanya zaben shugaban kasa dana ’yan majalisun tarayya a Asabar 20 ga Fabrairu 2027, da kuma na gwamna da ’yan majalisun Jihar a Asabar 6 ga Maris 2027.
Hukumar ta ce duk da cewa jadawalin ya yi daidai da tanade-tanaden doka, ta lura da damuwar masu ruwa da tsaki kan dacewar ranakun da watan Azumin Ramadan, don haka tana ci gaba da tuntuba, tare da yiwuwar neman matakin da ya dace bisa tsarin doka.
INEC ta jaddada kudurinta na tabbatar da zabe na gaskiya, sahihi da hada kan al’umma, tare da alkawarin sanar da jama’a duk wani ci gaba a kan lamarin.
You must be logged in to post a comment Login