Connect with us

Labarai

INEC ta samar da na’u’rorin zamani don bayyana sakamakon zaben Imo

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta samar da na’u’rorin zamani na musamman da za ta yi amfani da su wajen bayyana sakamakon zaben sanatan yankin Arewa a Jihar Imo, wanda za a yi a ranar talatin da daya ga watan gobe na October.

Shugaban hukumar na Jihar Farfesa Francis Ezeonu ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema Labarai a Jiya Litinin.
Ezeonu ya kuma ce, hukumar ta INEC ta shirya gudanar da zaben yadda ya kamata ba tare da samun wata matsala ba.

Ya kuma ce hukumar za ta fara tattaunawa da ma’aikatan da za su gudanar da aikin zaben daga lokacin da aka fitar da sunayen su daga ranar goma sha Bakwai ga watan da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,772 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!