Connect with us

Labarai

Magudin zabe : Amurka ta sanya takunkumin hana biza ga wasu ‘yan Najeriya

Published

on

Gwamnatin Amurka ta ce ta sanya takunkumin hana biza ga wasu mutane sakamakon aikata magudi a lokacin zaben jihohin Kogi da Bayelsa a Najeriya.

Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo.

Mista Pompeo, ya ce za a dauki irin wannan mataki a kan duk wanda aka samu da aikata magudi a zabukan jihohin Edo da Ondo da za a yi a watan Satumba da kuma Oktoba.

Gwamnatin Amurka ta ce duk da laifin da mutanen suka aikata, amma an nade hannu an zuba musu ido, ba tare da an dauki mataki a kan su ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,771 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!