Labarai
INEC ta tura kayan zabe zuwa kananan hukumomi 21 na Anambra

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta rarraba kayan zabe zuwa kananan hukumomi 21 na jihar Anambra, a kokarinta na fara shirin gudanar da zaben gwamna da za a gudanar gobe Asabar.
Shugabar hukumar ta jihar Anambra, Queen Elizabeth Agwu, ce, ta tabbatar da hakan yayin da jami’an tsaro da wakilan jam’iyyun siyasa suka halarci rabon kayan a cibiyar ajiyar kayan zabe ta jihar.
Ta ce hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya, adalci, da kwanciyar hankali.
INEC ta kuma tabbatar wa jama’a cewa an dauki matakan tsaro masu karfi domin kare kayan zabe da tabbatar da cewa ‘yan kasa sun kada kuri’unsu ba tare da tsoro ba.
You must be logged in to post a comment Login