Labarai
INEC za ta gana da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, za ta gana da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar adawa ta PDP yau Talata dangane da taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga watan nan da muke ciki na Yuni.
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta INEC ta mika wa shugaban jam’iyyar ta PDP Ambasada Umar Damagum.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan takaddamar da ta kunno kai a tsakanin hukumar da kuma jam’iyyar ta rashin bin ka’idojin gudanar da taron na PDP.
You must be logged in to post a comment Login