Labarai
INEC:Ta ce tana dakon hukuncin babbar kotu kan zaben Zamfara
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce tana dakon hukuncin da babbar kotu zata yanke kan zaben fida gwani na jam’iyyar APC dake jihar Zamfara ska yi.
Kwamishinan zabe kuma shugaban kwamitin ilimantarwa da wayar da kan masu yin zabe na kasa Festus Okoye ne ya bayyana hakan a babban birnin Tarayya Abuja ewa hukumar INEC din na bin dokoki sau-da-kafa.
A cewar Festus Okoye hukumar ta INEC zata cigaba da rike takardar shedar zababban gwamnan jihar ta Zamfara da aka zabe Alhaji Mukhtar Shehu biyo bayan jiran sakamakon hukuncin da babbar kotun tarayya zata yanke dake jihar Sokoto.
Sai dai jam’iyyar APC da zababban gwamnan jihar ta Zamfara Alhaji Mukhtar Shehu a cikin wani kunshin wasika da ya aikewa hukumar ta INEC a makon jiya, ta ce babbar kotun tarayya bata soke zaban fidda gwanin ba na jihar Zamfara.
Akan haka ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce, ta cire sunan dan takarar jihar Zamfara daga cikin jerin sunayen wadanda zata baiwa takadar shedar zaban gwamnan kasancewar ana zargin cewar bata gudanar da zaben fidda gwani ba.