Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu dauki mataki akan jami’anmu dake hada kai da ‘yan siyasa -Hukumar kula da shige da fice

Published

on

Zamu dauki mataki akan jami’anmu dake hada kai da ‘yan siyasa -Hukumar kula da shige da fice

Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa, Muhammad Babandede ya ce hukumar su a shirye take domin daukar tsatsauran mataki akan duk wani jami’in ta da ta kama da laifin kulla alaka da wani dan’ siyasa ko mai hannu da shuni wajen karya dokar Hukumar.

Muhammad Babandede ya Kara da cewa sun sami labarin cewa Yanzu jami’an su basa bincikin yan’siyasa ko musu hannu da shuni a lokacin da suke kokarin ketaro iyakar kasar nan.

Muhammad babandede ya bayyana hakan ne lokacin da ake Karin girma ga masu taimakawa Kwantrola janar guda goma sha hudu da akayi jiya A birnin tarayya Abuja.

Haka kuma yace kimanin Mutane Goma Sha biyar Ne Hukumar zata hukunta bisa zarginsu da mabambanta laifuka.

Muhammad Babandede ya kuma shawarci sababbin masu taimaka masa dasu sanya ido Akan jami’ansu domin yin aiki kamar yanda yake.

A cewar sa ya zuwa Yanzu akwai masu hannu da shuni da yan’siyasa da suke tunanin  zasu yi yin komai da kansu, batare da zuwa offishin  hukumar hana fasa kauri ba.

A don haka yake   kira da babbar murya kancewa duk wanda suka kama da irin wannan laifin ba shaka zasu dauki mataki akan sa.

LABARAI MASU ALAKA:

Hukumar hana fasa kwauri ta kama wasu motocin alfarma 18

An kawo gawar jami’in hukumar fasakwauri Nura Shu’ibu Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!