Labarai
Inganta muhalli: gwamnatin Kano ta ƙaddamar da dasa bishiya miliyan ɗaya
A wani mataki na magance matsalolin da muhalli ke fuskanta, gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da dashen bishiya miliyan ɗaya a faɗin jihar.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya ƙaddamar da dashen bishiyar kashi na farko a titin gidan gwamnati.
Yayin ƙaddamarwar Getso ya ce “Mun lura cewa dasa bishiya shi ne babban tsanin da zai magance mana matsalar muhalli, da kuma samar da ingantacciyar lafiya ga al’umma, wannan ne ya sanya a bana muka ɗauki matakin dasa bishiya miliyan ɗaya”.
Ko da aka tambayi Kwamishinan cewa a bara gwamnatin ta dasa bishiya miliyan biyu, ko me yasa a bana aka samu ragi? sai ya ce “Wannan shi ne babban ci gaban da muka samu a bangaren dasa bishiya domin kuwa akwai ƙungiyoyi da hukumomi dama da suka bada gudunmawa wajen dasa bishiya a bana kimanin miliyan 2 dalilin kenan da ya sa a banan za mu dasa miliyan 1”.
“Rashin wadatattun bishiyoyi na barazana wajen ƙonewar dama-daman da muke da su da kuma zaizayar ƙasa da ambiyar ruwa, sai kuma ɗumamar yanayi, wanda a bara bincike ya nuna cewa Kano ta fuskanci ɗumamar yanayi da ya kai ma’aunin salshiyos 44 hakan ya nuna cewa a bana an samu raguwar sa” in ji Getso.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, gwamnati ta yi haɗin guiwa da wani kamfani da zai taimaka wajen dasa bishiyoyi a Kano, inda nan ba da jomawa ba gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai ƙaddamar da dashen bishiyar kashi na 2.
You must be logged in to post a comment Login