Connect with us

Labarai

Ganduje zai dasa Bishiyu miliyan biyu domin kiyaye zaizayar kasa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace za ta gudanar da dashen bishiyu guda miliyan biyu a sassan jihar Kano don kiyaye kwararowar hamada da Kuma barazanar zaizayar kasa.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a yau, yayin bikin ranar muhalli ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, a yanzu haka ma’aikatar muhalli ta mayar da hankali wajen kula da dam-dam da ke jihar Kano tare da Samar da hanyoyin da za a rika zubar da  dagwalon masana’antu a yankunan chalawa da sharada da Kuma bompai ba tare da sun gurbata muhalli ba.

Ko kun san halin da Al’ummar Tofa suka shiga anan Kano

Majalisar dokokin jiha zata magance matsalolin muhalli

Ya Kara da cewa, da zarar an yi nasarar kawar da cutar corona, ma’aikatar muhalli za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaftar muhalli da take yi a yanzu don yaki da sauran cututtuka a jihar Kano.

Kabiru Ibrahim Getso ya kuma yi Kira ga jama’a da su rika tsaftace muhallan su, tare da gujewa dabi’ar sare bishiya ba tare da an mayar da madadin ta ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,853 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!