Labarai
ISWAP ta rabawa jama’a kudade a Borno
Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addar ISWAP sun raba wa jama’a makudan kudade a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno na jihar dake a yankin Tafkin Chadi.
Rabon kudin dai na zuwa ne bayan babban bankin kasa CBN ya tsawaita wa’adin ci gaba da amfani da tsaffin kudade zuwa Kwanaki 10.
An tabbatar da cewar ‘yan ta’addar sun tsaya akan titi dauke da buhunhunan tsaffin kudin da suka kunshi Naira 200 da 500 da kuma 1000 suna rarrabawa matafiyan da ke a kan hanyar.
Shaidun gani da Ido sun bayyanawa cewar ‘yan ISWAP din da suka yi shigar kayan Sojoji tare da girke motocin sulke guda 2 akan hanyar inda suke tare motocin suna bin fasinjojin daya bayan daya da kyautar tsaffin kudin a babbar hanyar da ke karamar hukumar Guzamala.
Guda daga cikin fasinjan da ya riski rabon kudin ya shaidawa manema labarai cewa mayakan na ISWAP sun baiwa kowanne fasinja da ke cikin motar kudin da yawansu ya kai dubu 100.
Rahoto: Aminu Halilu Tudun Wada
You must be logged in to post a comment Login