Manyan Labarai
Iyalan mutumin da aka cinna wa gidansa wuta a Gayawa sun nemi dauki
Iyalan mutumin nan da wasu bata gari suka kashe ta hanyar banka wa gidansa wuta a unguwar Gayawa a karamar hukumar Ungogo a nan Kano, sun nemi agajin mahukunta da su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an yi musu adalci ,a bincike da kuma shari’ar da ake yi kan wadanda ake zagin sun hallaka shi.
Tun dai a kwanakin baya ne wasu suka shiga cikin gidan marigayin wanda dan kasuwa ne, suka cinna wa gidan wuta inda hakan ya yi sanadin mutuwar magidancin da ‘yarsa daya da matarsa mai dauke da juna biyu.
Bayan da bincike ya yi nisa ne sai jami’an ‘yan sanda suka kama wani matashi mai suna Salisu Idris dan shekara 20, wanda ya tabbatar da cewa tabbas da shi aka je gidan amma dai ba shi ne ya kunna wutar ba.
Sai dai bayan kara matsa bincike da ‘yan sandan suka yi ne sai suka gano akwai wani matashi mai suna Alhaji Ta Kano wanda ke da alaka da aikata kisan inda shi ma suka shiga nemansa, bayan da aka tsegunta musu cewa ya gudu garin Asaba na jihar Delta.
Amma ko da jami’an ‘yan sandan suka yi yunkurin kama shi a garin basu samu nasara ba kasancewar ana zargin mahaifinsa ya sanar da shi zuwan jami’an tsaron domin kama shi.
Hakan ce kuma ta sa jami’an ‘yan sandan suka kama mahaifin nasa tare da gurfanar da shi a gaban kotu, inda kotun ta bada belinsa.
A cewar iyalan mamacin, suna bukatar gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, da sauran mahukuntan jihar Kano da su sanya baki wajen ganin an bi musu hakkin ran dan uwansu.