Labaran Kano
Iyaye sun bukaci gwamna Ganduje da a dawo musu da ‘yayansu da aka sace
Iyaye da dama ne suka halarci hukumar da ke binciken dangane da matsalar yawan sace-sacen yara da ake yi fama da shi a jihar kano, ake kuma sayar da su jihar Anambra.
Rahotannin na nuni da cewar hukumar karkashin jagorancin alkali Wada rano na zaman sa ne a babban kotun da ke haramar titin Miller da ke kwaryar Kano.
Iyeyn dai sun bukaci gwamnatin jihar Kano da ta yi hubbasa wajen ceto sauran yaran da har kawo yanzu ba’a kai ga gano inda suke ba.
Sun bayyana wa zaman hukumar cewar mafi yawan wadannan yara da suka bata ya faru ne tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2017.
Wata mahaifiya ‘yar shekara 39 , kuma mahaifiya ga ‘yaya biyar Zainab Ibrahim cewar ta yi ‘danta Ja’afar dan shekara 4 dai ya bata ne a unguwar Brigade tun shekara ta 2017 har kawo yanzu ba’a san inda yake ba.
Sai kuma kuma wasu iyayen da suka ce ‘dan sa Kamaludeen Lawan mai shekaru 3 da haihuwa shima ya bata ne a shekara ta 2017.
Jaridar Kano focus ta rawaito wani uba Zahradeen Lawan shima dan shekara 33, ya bayyana cewa ‘dan sa ya bata ne a yayin taron wani bikin aure yayin da ya tafi da mahaifiyarsa.
Sai wata batar na wani malamin makaranta Sunday Omole da yayi tun watan Mayun shekara ta 2018 mai shekaru 31, malami kuma a matakaranta gwamnati ta FGC Kano.
Firincifal fin makaranta Mrs Dangana dai ta ce an kawo mata labarin batan Omole ne inda ta ke ciki da bacin rai.
Al’amarin bai tsaya ga ‘yan asalin jihar Kano kadai ba, Sunday Omole dan jihar Benue da ke koyar da ilimin komputa wanda aiki ne ya kawo shi nan jihar Kano
Idan dai za’a iya tunawa dai gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje dai ya kaddamar da hukumar ne domin binciken yawaita sace-sacen mutane da ake yi a jihar musammam ma satar yara.
Hukuncin da gwamna Ganduje dai ya yanke ga wadanda suka sace yara goma da aka ceto su a jihar ta Anambra aka kuma canza musu adini zuwa na Krista tare da sauya musu sunaye iri na kabilar Igbo.