Labaran Kano
Iyayen yaran da aka sace sun bukaci taimakon al’umma
Iyayen yaran da aka sace a sassan uguwannin Hototo da kewaye a nan Kano sun bukaci al’umma da su taya su da addu’ar neman Allah ya bayyana sauran yaran da har yanzu ba a kai ga gano su ba Onitsha ta jihar Anambra.
A cewar wasu daga cikin iyayen yaran yara 49 ne suka bata inda zuwa yanzu aka gano 9 daga cikin su a garin Onitsha na jihar Anambra, bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta jagoranci wani aiki ne nemo yaran.
A zantawar Freedom Radio da Sakataren kungiyar iyayen yaran da ake zargin an sace din Attajiri Hotoro, ya bayyana cewa yanzu haka suna da kalandar hotunan yaran da suka batan su 49 inda ya kara da cewa yanzu haka akwai maganar cewa za a koma domin sake lalubo sauran yaran.
Shi kuwa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Malam Ahmad Iliyasu, ya bayyana cewa sun fara binciken ne kan wani mai suna Paul da aka kama da wani karamin yaro yana yunkurin ficewa da shi daga jihar Kano.
Kwamishinan ya kara da cewa, bayan sun matsa shi da tambayoyi ne ya shaida musu inda suke kai yaran.