Labarai
Jagoran adawar Kamaru Issa Bakary ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasa

Jagoran adawar kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi.
Cikin wani bidiyo da ya fitar, da tsakar daren da ya gabata, Bakary ya gode wa al’ummar Kamaru kan yadda suka samar da canji da ya ce sun yi a ƙasar, iƙirarin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓukan.
Bakary ya ce, cikin girmamawa da nutsuwa al’ummar Kamaru sun yi zaɓinsu, don haka ya kamata a martaba zaɓinsu, da ya alƙawarta wallafa cikakken sakamakon zaɓukan daga rumfunan zaɓen ƙasar.
Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba game da iƙirarin jagorar adawar, to amma a baya ministan cikin gida na ƙasar, Paul Atanga Nji ya nanata haramcin iƙirarin nasara daga ɗaiɗaikun ƴantakara tare da wallafa abin da ya kira haramtaccensakamakon zaɓe.
You must be logged in to post a comment Login