Labarai
Rahoto: Jama’ar unguwa na gina wa kansu kwalbati ta kusan N5m a Kano
Al’ummar wasu unguwanni a nan birnin Kano sun yi haɗin gwiwa wajen sake sabinta kwalbatin da ta haɗa yankunansu.
Unguwannin sun haɗar da Darma da Dukawa da Zangon bare-bari da kuma wani ɓangare na unguwar Sharifai.
A ziyarar da Freedom Radio ta kai unguwannin ta iske yadda aikin yayi nisa.
Malam Mubarak Abba na cikin matasan unguwar da suka assasa gudanar da wannan aiki, ya ce daga yanzu sun daina jiran gwamnati tayi musu irin wadannan aikace-aikace.
Nawa za a kashe wajen kammala aikin?
Mubarak Abba yace, sun gudanar da ayyukan ci gaban unguwa da dama amma wannan shi ne mafi girma da suke yi.
Ana sa ran aikin zai lashe kuɗi har kimanin miliyan biyar.
Labarai masu alaka
Gwamnatin Kano zata dauki matakai tsaurara kan wandada ke kin tsaftace muhallan su
Gwamnatin Kano ta kawo mana dauki – Al’ummar Faggen-Kankara
Yadda ake samar da kuɗin aikin
Mutanen yankunan na tattara kuɗi-kuɗi a tsakaninsu inda kowa ke bada abin da Allah ya hore masa don gudanar da wannan aikin.
A cewar Muhsin Aminu Dukawa wanda ke tattara kudin aikin.
Iyaye mata na bada tasu gudummuwar
Iyaye mata ma ba a barsu a baya ba, wajen bada tasu gudummuwar.
Hajiya Fadima Danbalarabe wadda aka fi sani da Niniya tana cikin iyaye mata a yankin.
Ta ce, su na bayar da abinci ga masu aikin da sabulan wanke jiki da duk wani abu da Allah ya hore musu.
Yaya manyan unguwannin suka karɓi aikin?
Matasan da suka jagoranci aikin sun ce wannan aiki bai samu ba sai da gudummuwar masu unguwanni da dattijan yankin.
Alhaji Lamin Isah na cikin dattawan unguwannin yace wannan kwalabati ta daɗe tana ci musu tuwo a kwarya, amma yanzu ƴaƴansu sun tasamma magance musu matsalar ta.
Malaman Addini sun shigo cikin aikin
Da yake unguwannin sun yi shura da al’amuran addini ya sanya matasan suka sanya malaman addinin yankin kan gaba wajen gudanar da shi.
Gwani Hadi Sadisu Zangon Bare-bari fitaccen malamin alkur’ani ne a nan Kano wanda ke cikin wannan aiki.
Ya ce, yana farin ciki sosai yadda matasan unguwar suka neme shi matsayin mai bada shawarwari kan gudanar da aikin.
Yaya al’umma ke kallon aikin?
Masu kishin al’umma dai na cewa wannan shi ne abin da ya kamata al’umma su rika yi domin kawo ci gaba a yankunansu.
Alhaji Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Gwamnati Ikon Allah ɗaya ne cikin masu kishin al’umma a Kano.
“Muna kira ga sauran matasa da su yi koyi da waɗannan unguwanni saboda in an tsaya jiran gwamnati za a jima gyaran bai samu ba”.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum dai sun jima suna kalubalantar gwamnati kan yadda kusan kowacce unguwa ke fama da irin wannan matsaloli, kuma gwamnati ta kasa gyarawa har ta kai ga al’umma sun fara daukar irin wannan mataki na gyarawa da kansu.
Ku kalli rahoton cikin bidiyo.
You must be logged in to post a comment Login