Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano zata dauki matakai tsaurara kan wandada ke kin tsaftace muhallan su

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata dau matakai tsaurara kan duk wanda ta sake kamawa da bujirewa na kin tsaftace muhallansu ko harabar sana’arsu.

Babban Sakataren ma’aikatar muhalli na jihar Kano Alhaji Ibrahim Halilu Dan-Tiye ne ya bayyana hakan yayin ran-gadin duba tsaftar muhalli na karshen wata.

Dan-Tiye yace,  a zagayen da tawagar ta yi , masu ababen-hawa da dama da dai-daikun mutane  sun fito suna ta hada-hada su a maimakon tsaftace muhalli.

Wasu daga cikin mutane da aka ci su tara sun bayyana nadamarsu tare da neman afuwar Gwamnati.

Babban Sakataren ya kuma ja hankalin al’umma da su kasance masu bin doka da oda don kaucewa hukunci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,481 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!