Labarai
JAMB na da hurumin samar wa dalibai guraben karatu- Gwamnatin tarayya

Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, karkashin Ministan ilimi Dakta Maruf Tunji Alausa, ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa hukumar sharya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da Sakandare ta JAMB ba ta da ikon sama wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu a fadin Najeriya.
Wata sanarwa da Ma’aikatar ta fitar, ta bayyana cewa irin waɗannan rahotOnni ba su da tushe balle makama, kuma suna iya rikita jama’a da ɗalibai musamman masu shirin shiga manyan makarantu.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa hukumar JAMB na da cikakken hurumi da doka ta bata wajen gudanar da jarrabawar shiga jami’a, tare da tabbatar da daidaito da inganci a tsarin karɓar ɗalibai
You must be logged in to post a comment Login