Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

JAMB na shirin sama wa daliban da suka dawo daga Sudan makoma

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu JAMB, ta ce, za ta samar da guraben karatu ga daliban da rikicin kasar Sudan ya rabo da karatunsu.

Shugaba hukumar farfesa Ishaq Olayede, ne sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, kwana guda bayan wata ganawa tsakanin shugabannin hukumar ta JAMB da shugabar hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen ketare Abike Dabiri Erewa.

Farfesa Ishaq Olayede, ya kuma bukaci daliban da su tabbatar sun bi ka’idojin da hukumar ta samar domin samun damar ci gaba da karatun su a gida Nijeriya.

Haka kuma, ya bukaci kada a halin ko-in-kula da daliban da rikicin kasar Ukraine ya shafa na yin shakulatun bangaro da karatunsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!