Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an EFCC sun garƙame gidan Yahaya Bello domin cafke shi

Published

on

Da tsakar ranar yau Laraba ne jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC suka yi wa ƙofar gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello tsinke da nufin cafke shi.

Rahotonni sun bayyana cewa, jami’an na EFCC, sun yi amfani da gwamman motocinsu wajen rufe layin gidan tsohon gwamnan wanda ya ke a Benghazi Street a Wuse Zone 4 da ke birnin tarayya Abuja.

Haka kuma jami’an sun hana masu wucewa yin amfani da hanyar har zuwa kammala aikinsu.

Sai dai, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa akwai yiwuwar yunƙurin cafke Yahaya Bello ba shi da nasaba da tuhumar da hukumar ke masa ta almundahanar Naira Biliyan 48.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!