Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta sanya ranar ci gaba da shari’ar Ganduje da PCACC ta shigar

Published

on

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 4 ƙarƙashin mai Shari’a Usman Na’abba ta soma sauraron ƙarar da Gwamnatin Kano ta shigar da Tsohon Gwamna Ganduje da wasu mutane.

Yayin zaman Kotun lauyoyin waɗanda ake ƙara sun bayyanawa Kotun cewar masu ƙara ba su shirya ba domin sun gaza sadar da sammaci ga waɗanda ake ƙara duk da shari’ar ta laifi ce.

A nan ne lauyoyin Gwamnati suka roƙi Kotun ta yi umarni da wadanda ake ƙara su zo gabanta, sai dai Lauyan masu kariya roki kotu ta yi watsi da rokon inda ya ce irin wannan shari’ar sammaci kawai ake kai wa ba sai Kotu ta ba da umarni ba.

A ƙarshe Kotun ta sanya ranar 29 ga watan Afrilun da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.

Gwamnatin Kano ta hannun Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano ce ta yi ƙarar Tsohon Gwamnan da wasu mutane ciki har da matarsa da ɗansa bisa zargin sayar da kadarorin Gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, da wadaƙa da dukiyar jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!