Labarai
Jami’an Hisbah sun karbi horo kan kokawar Karate a Kano
Hukumar Hisbah ta Kano tace an kammala horas da jami’an ta dari biyu dabaru kan yadda kowanne jami’i zai iya fada da mutum biyar batare da yayi amfani da makami ba.
Hukumar ta Hisba ta dauki matakin ne domin jami’an su dinga kare kansu daga farmakin batagari musamman idan sun kai sumame.
Babban Kwamandan Hukumar ta Hisbah Malam Harun Ibin Sina ne ya bayyana haka a yau lokacin da Kungiyar Kano State Karate Association ta kammala horas da jami’an hukumar dari biyu dabaru kan yadda zasu kare kansu daga farmaki.
Ibin Sina ya kara da cewa irin sabbin dabarun da aka koyawa jami’an hukumar Hisbah abun mamaki ne musamman yadda suke iya lankwasa jikinsu su yi abubuwa na ban al’ajabi da kuma yadda suke iya yin tsalle – tsalle.
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar na yankin Arewacin Najeriya Malam Salisu Ibrahim mai Lakabin suna Shehan yace yanzu haka sun koyawa jami’an hukumar dabaru wajen iya fada da mutane da hannu ba tare da sun yi nasara akansu ba.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito an baiwa jami’an lambar girmamawa kuma babban kwamandan Ibin Sina na cewa sun shirya tsaf domin sake tura wasu jami’an hukumar ta Hisbah mutum dari biyu domin suma a koya musu sabbin dabarun na kare kai.
You must be logged in to post a comment Login