Labarai
Jami’an tsaro na buƙatar samun bayanan sirri daga al’umma – Manjo Kabiru Imam
Rundunar ta ɗaya ta sojojin ƙasa da ke Kaduna ta buƙaci da riƙa kai rahoton maɓoyar ƴan bindiga ga jami’an tsaro.
Kwamandan rundunar Manjo Janar Kabiru Imam Muktar ne ya buƙaci hakan a ziyarar da ya kai gidan gwamnatin Kano a wani ɓangare na ziyarar aiki da yazo yi Kano.
“Mun zo mu duba yadda harkar tsaro yake kuma mu ga yadda suke gudanar da ayyukan su da kuma abubuwan da suke buƙata”.
“Dajin Falgore na ɗaya daga cikin guraren da muka ziyarata inda ya zama sansanin harar da jami’an tsaro, kuma idan za a tuna dajin ya daɗe yana zama barazana ga al’umma dalilin rashin tsaro” a cewar Manjo.
Ya kuma ce, harkar tsaro ba aiki ne na jami’an tsaro kaɗai ba, lamari ne da ya shafi kowanne ɗan ƙasa.
“Mutanen Kano na karɓar baƙi daga ko’ina don haka kamata yayi su rika bukaci da a riƙa sanya idanu a kan bakin da ke shigowa don sanin waɗanne irin mutane ne ke shigowa tare da ta tabbatar da cewa ba mugaye ba ne” in ji Manjo Janar Kabiru.
Ya ƙara da cewa, jami’an tsaro na buƙatar samun labarun maɓoyar masu aikata laifi wanda hakan zai taimaka wajen daƙile matsalolin tsaro a ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login