Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An umarci ‘yan sanda su zama cikin shirin kota kwana a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi jami’anta da su zamo cikin shirin kota kwana, musamman masu aiki kan hanyar Kano zuwa Kaduna da wadanda ke hanyar Kano zuwa Plato, a yankin dake kusa da dajin Falgore.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu Sani ne yayi wannan umarni lokacin da yake ziyarar aiki domin ganawa da jami’an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki a fannin tsaro a wadannan yankuna da yammacin jiya Lahadi.

Ya kuma umarce su da su kasance masu yin aiki dai-dai da tanadin doka,

A yayin ziyarar garin Doguwa dake kan hanyar Kano zuwa Plato, hakimin Doguwa Dan adalan Rano Alhaji Abdullahi Iliyasu ya yabawa kwamishinan bisa kokarin sa na kawo ‘yan sandan da suka kakkabe masu aikata laifuka a dajin na Falgore

Hakimin yace, nasarar da aka samu a jejin na Falgore ya biyo bayan fahimtar juna da aiki tare da aka samu tsakanin yan sintirin yankin da ake kira ‘Yan Bula da kuma jami’an ‘yan sanda.

Karin labarai:

‘Yan sanda sun cafke dillalan miyagun kwayoyi sama da 1,000 a Kano

‘Yan sanda sun nemi Buhari ya samar da kotun hukunta masu fyade

Shima ansa bangaren shugaban ‘yan sintiri na yan bula Malam Haruna Adamu ya nuna farin ciki ne bisa wannan ziyara da kwamishinan ya kai jejin na Falgore, yana mai cewar jeji ne mai hatsari wanda ya hada Kano da Bauchi har zuwa jejin Sambisa.

Wata takarda mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP. Haruna Kiyawa ta bayyana cewar kwamishina Habu Sani ya bayyana matukar jin dadinsa bisa yadda yaga abubuwa na tafiya a yankin ya kuma shawarci al’ummar yankin da su karfafawa matasan su masu kishi kan su shiga cikin masu aikin ‘yan sanda da ake shirin fara dauka domin su dawo su hidimtawa al’umar su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!