Labarai
Jami’an tsaro sun kama mota dauke da karafunan titin jirgin kasa

Hukumar tsaron Civil Defence a Jihar Bauchi ta kama wata babbar mota da ke ɗauke da layukan dogon jirgin kasa da ake zargin an sato, tare da kama mutane biyar da ake zargi da aikata laifin.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf, ya fitar ta ce, an cafke motar ne bayan samun bayanan sirri, a hanyar Miri zuwa Jos, kusa da Gital a ƙaramar hukumar Tafawa Balewa, yayin da ake ci gaba da neman direban motar da sauran masu dakon kayan da suka tsere.
Kwamandan na Civil Defence a jihar, Oloyede Nelson, ya jaddada ƙudirin hukumar na kare muhimman kadarorin ƙasa tare da yaƙi da ɓarna, yana mai kira ga al’umma su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai duk lokacin da suka ga motsi da basu aminta da shi ba.
You must be logged in to post a comment Login